A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ofishin Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani ya sanar da rasuwar wannan marja’in ta hanyar fitar da sanarwa.
Ga cikakken bayanin sanarwar kamar haka:
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai
«الَّذِینَ تَتَوَفَّاهُمُ الْمَلَائِکَةُ طَیِّبِینَ ۙیَقُولُونَ سَلَامٌ عَلَیْکُمُ ادْخُلُوا الْجَنَّةَ بِمَا کُنْتُمْ تَعْمَلُونَ»
“Waɗanda mala’iku suke karɓar rayukansu alhali suna cikin tsarki, suna ce musu: Amincin Allah a gare ku. Ku shiga Aljanna saboda ayyukan da kuka kasance kuna aikatawa.”
Tsarkakakken ruhin malamin fikihun Ahlul Baiti (A.S), kuma babban marja’in duniyar Shi’a, Ayatullahil Uzma Shubairi Zanjani (Allah Ya jiƙan sa da rahamarSa), ya hadu da Ubangiji.
Rayuwa mai albarka da tarihin wannan babban marja’i sun kasance cike da zurfin tunani, da ci gaba da gwagwarmayar ilimi, da ƙoƙari na gaskiya wajen kiyaye da ɗaukaka ingantaccen ilimin fikihu, da yaɗa koyarwar Musulunci, da kare ginshiƙan mazhabar Shi’a, tare da nuna kyakkyawar niyya da kulawa ga al’umma.
Muna miƙa saƙon ta’aziyya bisa wannan babban rashi mai raɗaɗi ga fiyayyen halitta, Ma’abocin Al’amari, Hazrat Baqiyyatullahi al-A’zam (A.F), da makarantu masu albarka na ilimin Hauza, da al’ummar Iran masu daraja, da kuma dukkan masu ƙaunar jagorancin marja’iyya a sassa daban-daban na duniya.
Haka kuma, muna sanar da cewa za a bayyana lokacin da wurin gudanar da jana’izar da binne gawar wannan malami mai daraja a nan gaba.
Daga cikin manyan malaman ɗaliban wannan babban marja'i akwai Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamene'i (Dz)
Ra'ayinka